Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Shafin yanar gizo na labarai ‘Africanews’ ya bayyana cewa a taron kwanaki biyu wanda aka fara yau kasashen nahiyoyin biyu zasu tattauna batutuwa da suka hada da matsalolin cutar Covid19, kwarar ‘yan gudun hijira zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya, juye-juyan mulki a wasu kasashen yankin, da kuma iran yadda kasashen Rasha ta China suke kutsawa cikin nahiyar ta Afirka.
Shugaban kasar Snegal wanda ya sami halattan taron ya bayyana cewa bukatun kasashen Afirka sun ne a sake sabon lale kan yadda wadannan kasashen suke hulda da kasashemmu, a sabonta yanayin hulda da kasashen Afirka ta yadda zai zama na zamani.
A bangaren kasashen Turai kuma suna son nunawa shuwagabannin kasashe 40 na nahiyar Afrika da suka sami halattan taron kan cewa Turai tafi masu kasashen gabas. Daga cikin shirin nasu akwai na zabu jari mai yawan dalar Amurka biliyon 170 a nahiyar a cikin shekaru masu zuwa.
342/